Hauza/ Cibiyar Albasira Qom Karkashin Jagorancin Imam Sayyid Ibraheem Yaaqub Zakzaky (H) ta rufe taron zamammakin jajen Shahadar Shugabar matan duniya, Sayyida Fatimatuz-Zahra (SA) a Masallacin Bilal, Shahrek Mahdiye.

Acewar cibiyar Labarn Hauza, Ranar Litinin bayan Sallar Magriba da Isha,3 ga Jimada Thani, 1447, Cibiyar Albasira ta rufe tarukan Jajen Shahadar Sayyida Zahra (as), an fara taron da karatun Alkur'ani mai tsarki daga dan uwa Ahmad Abba Nuhu, sai karanta ziyara wanda Sheikh Faisal Isah Richifa ya gabatar. Hujjatul Islam Sheikh Abdulhadi Isah Richifa ne ya gabatar da jawabi a taron na rufewar.


Tun da farko Mallamin ya fara da kawo irin butulcin da aka yi wa Manzon Allah tun ba a bizne gangar jikinsa ba. Mallamin ya ce cikin jerin abin alkhair Manzon Rahama ya kawo wa wannan al'umma, akwai kaeta daga shiga wuta, a fadin Allah (SWT) :"...Kun kasance kuna gab da fadawa wuta, sai ya tsamar da ku daga ita...."(3:103).

Mallamin ya kara da kawo kissar yadda aka tura runduna suka je gidan da idan Manzon Allah zai shiga sai ya nemi izni sannan ya shiga, amma wannan mutanen haka suka keta alfarmar gidan da ma'abota gidan, suka doki diyar Manzon Allah kana suka zubar mata da dan tayinta, har ta kai ga karya kashin awazinta, wanda hakan shi ya kai ga sanadiyyar shahadarta.


Sheikh Abdulhadi ya kara da kawo kissar zuwan Khalifan farko tare da rundunarsa gidan Imam Ali (AS) wanda hakan na cikin dalilan da suka sa Sayyida Zahra (SA) ta abbatar musu da tayi fushi da su, kuma har tayi wafati tana yin fushin da su.

Bayan kammala jawabin Sheikh Abdulhadi ne mawaka suka gabatar da waken juyayin shahadar Sayyida Zahra (SA).


Tun a watan da ya gabata ne dai cibiyar ta Albasira ta fara gabatar da zamammakin jajen wanda Mallama Zeenatudden Ibrahim ta gabatar da jawabi a wurin, sannan ta shirya maukibi tare da bajakolin hotunan shahidan Harkar Musulunci karkashin jagorancin Imam Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) inda a yau din kuma aka gabatar da zaman rufewa (khatama).

Daga Media Forum, Cibiyar Albasira Qom Karkashin Jagorancin Imam Sayyid Ibraheem Yaaqub Zakzaky (H).

IMG-20251124-WA0085.jpg

IMG-20251124-WA0073.jpg

IMG-20251124-WA0072.jpg

IMG-20251124-WA0070.jpg

IMG-20251124-WA0069.jpg

IMG-20251124-WA0068.jpg

IMG-20251124-WA0066.jpg

IMG-20251124-WA0063.jpg

IMG-20251124-WA0062.jpg

IMG-20251124-WA0060.jpg

IMG-20251124-WA0057.jpg

IMG-20251124-WA0055.jpg

IMG-20251124-WA0045.jpg

IMG-20251124-WA0043-1-.jpg

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha